Jami’an Hukumar Yaki da Fasakwauri ta Kasa (NCS) shiyyar jihohin Neja/Kogi, sun kama kunshin Tabarar Wiwi 317 mai nauyin kilogram 253.6 a hanyar Abuja-Lakwaja.
Hukumar ta ce, a kiyasce kudin kayan da ta kama din ya kai Naira miliyan 20.6.
Kwanturolan hukumar mai kula da shiyyar Neja/Kogi, Busayo Olugbemiga Badejo, ya ce “Da an yi sake kayan sun shiga al’umma, hakan zai ci gaba da haddasa aukuwar manyan laifuka.”
Tuni Badejo ya mika kayan ga Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) a Jihar Neja domin daukar mataki na gaba da ya dace.
Ya kara da cewa, duba da zaben 2023 ya karato kamata ya yi masu ruwa da tsaki su zama masu sanya ido kan lamurra tare da taimka wa jami’an tsaro da muhimman bayanai.
Ya ce abin takaici ne yayin da wasu ke kokarin gina kasa, wasu kuwa sun ba da himma wajen rusa ta.
A nasa bangaren, Kwamandan NDLEA a Jihar Neja, Barista Haruna Kwatishe, ya yaba wa jami’an Kwastam kan namijin kokarin da suke yi a bakin aiki don tsaftace kasar nan daga manyan laifuka da miyagun kwayoyi.
“Ina mai gargadin ‘yan siyasarmu da suke amfani da matasa wajen bangar siyasa ta hanyar sura musu miyagun kwayoyi da su shirya.
“Domin kuwa ba za mu kyale duk wani dan siyasa da ke amfani da matasa yana dura musu miyagun kwayoyi don cimma manufarsa ba.
“Su sani cewa za mu kama su mu tsare har zuwa karshen zabe,” in ji shugaban na NDLEA.