✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta kama tankar iskar gas cike da tabar wiwi

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi a Najeriya (NDLEA) ta kama wata tankar iskar gas da aka cika ta da buhunan tabar wiwi guda…

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi a Najeriya (NDLEA) ta kama wata tankar iskar gas da aka cika ta da buhunan tabar wiwi guda 511.

Hukumar ta ce buhunan tabar wiwin da nauyinsu  ya kai kilogiram 4,752, an dauko su ne daga Jihar Ondo zuwa Abuja domin rarraba ta ga mabuƙata.

Jami’an NDLEA sun kuma ta gano wata kungiyar masu safarar miyagun kwayoyi ta ƙasa da ƙasa a sassan Najeriya.

Akalla mambobin kungiyar dillalan kwayoyin da ke da alaƙa da kasashen Afirka ta Kudu da kuma ƙasar Thailand guda biyar ne aka kama a jihohin Legas, Abia da Anambra.

Dillalan kwayoyin sun shiga hannu ne sakamakon samamen tsawon makonni biyu da hukumar ta kai bayan da ta kama miyagun kwayoyi a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Jihar Legas.

A Jihar Bauchi kuma jami’an NDLEA da ke sintiri a kan hanyar Bauchi zuwa Jos sun kama wani dan shekaru 39 da kwalaben 595 na codeine, da kwayoyin tramadol, rohypnol da diazepam da yawansu ya kai guda 38,260.

Hakazalika wasu matsa masu shekaru 22 da kuma 25 dauke da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 207.1 sun shiga hannun hukumar a Zaria da ke jihar Kaduna ranar Litinin da ta gabata.

Sai wani matashi dan shekara 35 da aka kama da kwalabe 194 na maganin tari a unguwar Hotoro a Jihar Kano.

A Jihar Benue a ranar Afrilu an kama  wani da kunshin tabar wiwi guda 66 da nauyinta ya ka kilo 33.

Shugaban NDLEA Birgediya Buba Marwa ya jinjina wa dakarun hukumar tasa bisa wannan namijin ƙoƙari wurin zaƙulo da tabbatar da an kamo duk wani mai sha ko safarar miyagun ƙwayoyi a Najeriya.