Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), ta kammala gyara wata cibiya don kula da masu fama da shan miyagun ƙwayoyi a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH) da ke Kano, tare da miƙa ta ga asibitin domin amfanin jama’a.
Jami’in ECOWAS mai kula da shirin hana yawaitar shan miyagun ƙwayoyi, Dokta Daniel Akwasi Amankwaah, ya ce wannan cibiya na daga cikin ƙoƙarin ƙungiyar wajen rage yawaitar shan ƙwayoyi da kuma tabbatar da samun ingantacciyar kulawa ga masu buƙata.
- Tinubu zai sake zama shugaban ƙasa a 2027 — Akpabio
- ’Yan sanda sun ƙwato wa mutumin da aka sace kuɗin fansarsa a Kano
A yayin bikin miƙa cibiyar, Dokta Amankwaah, ya jaddada aniyar ECOWAS na yaƙi da matsalar shan miyagun ƙwayoyi, inda ta ce duniya ta ɗauki wannan matsala a matsayin wata babbar barazana ga lafiya da zamantakewa.
Ya bayyana cewa bayanan da Hukumar Bincike kan Amfani da Miyagun Ƙwayoyi a Yammacin Afirka (WENDU), ta fitar daga 2018 zuwa 2023 sun nuna ƙaruwar masu shan miyagun ƙwayoyi a yankin, duk da ƙarancin wuraren kula da su.
Saboda haka, ECOWAS ta ƙaddamar da wani shiri tun a 2019 domin taimaka wa membobints wajen kafa ko gyara cibiyoyin kula da masu shan miyagun ƙwayoyi.
Ya zuwa yanzu, an kammala cibiyoyi takwas a ƙasashe shida, inda Najeriya ta samu guda huɗu, yayin da ake ci gaba da aikin wasu uku.
Dokta Amankwaah, ya ce kammala wannan cibiya a AKTH zai taimaka wajen kula da marasa lafiya ta hanyar dabarun kiwon lafiya, wanda zai rage illar shan miyagun ƙwayoyi tare da inganta rayuwar jama’a.
Kwamandan Hukumar NDLEA a Kano, Ahmed Idris, ya ce wannan cibiya wata babbar nasara ce a yaƙi da shan miyagun kwayoyi.
Ya yi kira da a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomi domin cimma gagarumin nasara.
Shi ma Shugaban AKTH, Abdurrahman Abba Sheshe, ya yaba da wannan tallafi, inda ya ce cibiyar ba kawai al’ummar Kano za ta taimaka ba, har da maƙwabtan jihohi.