Hukumar Kwastam ta kama wasu makamai da kakin sojoji a tashar Tin-Can Island da ake zargin wasu tawagar masu aikata laifuka ne suka shigo da su cikin ƙasar nan ta ɓarauniyar hanya.
Daga cikin abubuwan da aka kama sun haɗa da kakin sojoji da miyagun ƙwayoyi irin su Colorado.
- Za mu mayar wa ’yan kasuwa kayan abincinsu da muka kwace —Kwastam
- Kwastam ta dakatar da yin gwanjon shinkafa
Makaman da aka kama sun haɗa da bindigogi masu sarrafa kansu da kuma wasu nau’in bindigogin.
Kodayake, har yanzu ana kan zayyana cikakkun bayanai game da kamen da hukumar ta yi, kamar yadda majiyoyi suka ce an ƙwato makaman ne a yayin da ake duba kayayyakin da aka shigo da su ƙasar.
Kawo yanzu dai ba a bayyana ko an kama wani da ake zargin da hannu a shigo da kayayyakin ba
Kame kayan na zuwa ne bayan wata takwas da hukumar kwastam ta kama makamai iri-iri 31 a tashar ta Tin-Can da Multi-Purpose Terminals (PTML) da ke Legas.
Kwanturolan hukumar ta Kwastam, Mista Adewale Adeniyi, ya shaida wa manema labarai a lokacin cewa an kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu wajen kama su.