✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam ta dakatar da yin gwanjon shinkafa

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta dakatar da shirinta na yin gwanjon shinkafar da ta kwace ga ’yan Najeriya.

Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta dakatar da shirinta na yin gwanjon shinkafar da ta kwace ga ’yan Najeriya.

Hukumar ta dauki matakin ne bayan wani turmutsitsin da ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai.

Lamarin dai ya faru ne a yayin rabon buhunan shinkafa mai nauyin kilogiram 25 a hedikwatar hukumar da ke yankin Yaba a Jihar Legas.

Kakakin Hukumar, Abdullahi Maiwada,  ya sanar a ranar Litinin cewa dakatarwar na daga cikin matakan da hukumar ta dauka na tabbatar da tsaron lafiyar ’yan Najeriya da kuma lalubo hanyoyin da ya kamata ta bi domin kada a karya lagon shirin.

A hukumar dai ta sanar cewa yi wa jama’a gwanjon shinkafar na daga cikin yunkurinta na saukaka wa jama’a matsalar yunwa da tsadar kayan masarufi da al’ummar ƙasar ke fuskanta.

A kan hakan ne ta fara rabon shinkafa mai nauyin kilogiram 25 a kan rangwamen farashi na N10,000 a Legas.

A cewar mai magana da yawun hukumar, buhunan shinkafar sun kare a lokacin rabon, lamarin da ya haifar da fargaba a tsakanin jama’a.

A sakamakon haka suka yi yunkurin shiga wurin da ake rabon, wanda haka ya yi ajalin mutane bakwai, ciki har da wata mace mai juna biyu.

Wasu da dama kuma sun jikkata a sakamakon turureniyar.

Hukumar dai ta jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa tare da yi musu addu’a.

Ta kuma bayyana cewa kudaden da ake biya na sayen shinkafar na zuwa kai tsaye ne zuwa asusun Gwamnatin Tarayya.