✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

BUA ya yi alkawarin karya farashin shinkafa

Abdul Samad mai kamfanin BUA ya ce suna tattaunawa da Dangote kan yadda za su karya farashin siminiti

Shugaban Runkunin Kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya bayyana shirinsa na karya farashin shinkafa a Najeriya, yana mai cewa nan gaba kadan wadanda suka saye shinkafar suka boye suna jiya ta yi tsada, za su tafka mummunar asara.

Dan kasuwar ya kuma bayyana cewa suna tattunawa da Shugaban Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, kan hanyoyin da za su bi domin ganin sun daidaita farashin siminti.

BUA ya bayyana haka ne a yayin ganawarsa da manema labarai jim kadan bayan wata ganawa da ya yi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Kasa.

“Farashin kayan abinci na saukowa a Najeriya kuma muna yin duk abin da za mu iya na ganin cewa mun mara wa gwamnati baya a kan hakan,” kamar yadda ya bayyana,

Ya ci gaba da cewa, “Kun san shugaban kasa ya dage harajin shiga da kayan abinci kamar shinkafa da masara da alkama da dawa.

“A lokacin farashinsu ya tsahi sosai; a bara sai dai kudin buhun shinkafa ya kai N100,000, alkama da fulawa suka kai N80,000, masara ta kai N60,000, taliya kuma kwali ya kai N20,000.”

Ya bayyana cewa abin da ke faruaw shi ne, mutane ke saye shansherar shinkafa a lokacin kaka su boye, daga baya su tsawwarala farashin.

“Idan kaka ta wuce sai su ninka farashin. Wanna shi ne matsalar, kuma ba manoma ke cin moriyar karin farshin ba, saboda tun da kaka sun riga sun sayar wa ’yan kasuwar da ton daya a kan N400,000 ko N500,000.

“Su kuma wadanda suka saye suka boye, da zarar kaka ta wuce sai su ninka kudin ton zuwa N500,000,” in ji BUA.

Ya bayyana cewa amma janye harajin shigo da abinci da gwamnati ta yi ya rikita lissafin masu boye abincin, kuma a halin yanzu sun fara kokawa saboda irin asarar da suke tafkawa.

Ya ce, “duk da cewa ya kamata mu kare manomanmu, amma kuma yana da muhimmanci mu fahimci cewa yawan al’ummar kasar nan ya kai mutum miliyan 250, kuma yawancinsu ana sayar musu da kaya da tsadar da ta wuce misali, a sakamakon abin da wasu tsirarun kamfanoni ko mutane ke yi.

“Muna fata zuwa karshen wannan shekara farashin shinkafa ba zai fi yadda yake a yanzu ba. Na tabbata da zarar lokaci ya yi manoma za su samu shinkafa a farashin da suka saba, kuma ba zai karu ba a kasuwa, saboda mutane sun shirin masu boye ta, kuma idan sun boyen ma, asara suke yi,” in ji dan kasuwan.

Game da tsadar siminit, BUA ya danganta matsalar a faduwar darajar naira a kan dala.