✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Najeriya sun koka kan rashin ingancin shinkafar Gwamantin Tarayya

Wadanda suka sayi shinkafar sun yi ikirarin samun kwari a cikinta kuma tana yin kumfa idan ana dafa ta, sa’annan idan ta nuna tana yin…

’Yan Najeriya da suka rabauta da sayen shinkafar kasar waje da Gwamnatin Tarayya ta karya farashinsa sun koka bisa rashin ingancin wata wadda ake sayarwa a Jihar Kogi.

Wadanda suka sayi rukunin farko na shinkafar sun yaba da ingancinta da dandanonta, wasu kuma na korafi a kan yanayi da kuma dandanon wadda suka samu daga wani kamfani daga wata kasar Asiya.

Wasu suka samu shinkafar mai matsala sun yi ikirarin samun kwari a cikinta kuma tana yin kumfa idan ana dafa ta, sa’annan idan ta nuna tana yin danko sosai, sabanin yadda aka san shinkafar kasar waje.

Wani dan kasuwar shinkafar cikin gida a Najeriya ya yi zargin rukunin shinkafar da ta samu matsalar ta jima a ajiye ne kafin a fito da ita, shi ya sa ingancin ya samu matsala.

Don haka ya shawarci masu saya da su shanya ta a rana kuma su wanke ta sosai sa’annan su dan turara ta domin dawo da ingancinta.

A gefe guda kuma wadanda da suka amfana da wani rukuni na daban na shinkafar gwamnatin sun yaba da ingancinta ta fuskar dandano da kuma yanayi.

Kawo yanzu dai hukumomi ba su ce uffan game da korafin da jama’a ke yi kan wannan lamari ba.