Wata mata da ta yi wa masu neman aikin gwamnati damfarar kudi sama da Naira miliyan 250 ta shiga hannun jami’an tsaro.
’Yan sanda sun cika hannu da wannan mata mai suna Iyabode Oluwafemi ne a Jihar Ondo bisa zargin karbar kudaden ta hanyar yaudarar mutane da ta yi wa alkawarin sama masu ayyuka a ma’aikatu da hukumomi da cibiyoyin gwamnati daban-daban.
A yayin da da yake magana kan wadda ake zargin a ofishinsa da ke Akure, babban birnin jihar, Kwamishinan ’yan sanda a jihar, Wilfred Afolabi, ya ce jami’an runduanr sun yi nasarar kama Iyabode Oluwafemi ne bayan yawan korafin da mutanen da ta damfara suka yi.
Ya bayyana cewa da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da ita gaban kotu domin yanke mata hukunci.
- An kama yarinya kan kashe jariri a sansanin ’yan gudun hijira
- An kama jami’in Hukumar NRC da laifin satar waya
Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin wadda ake zargin, amma kakakin ’yan sanda na Jihar Ondo bai amince da zantawa da ita ba saboda a cewarsa yin hakan zai iya janyo koma-bayan binciken da suke yi.
Yadda ake damfarar masu neman aikin gwamnati
Binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna ana samun karuwar matasa maza da mata da suka kammala karatu, da ke neman aikin gwamnati ta bayan fage, ko haramtattun hanyoyi.
Daga cikinsu akwai ’ya’yan masu madafun iko da iyayensu suke amfani da matsayinsu wajen tilasta ba su ayyukan gwamnati ga. Akwai kuma ’ya’yan masu masu kumbar susa da suke biyan kudaden da suka kama daga naira miliyan daya zuwa sama a matsayin na-goro domin sayen guraben aiki.
Marasa galihu kuma sukan yi kundumbala, inda wasu ke ciwo bashin kudi da gwanjatar da ’yan abin da su ko iyayensu suka mallaka domin cimma wannan buri, da alkawarin biya idan sun samu.
Wasu mata daga cikinsu sukan ba da kansu, ko su yi yawon karuwanci domin kawai su samun abin da za su yi domin samun aikin gwamnati.
A gefe guda kuma, akwai jami’an gwamnati da dillalai masu karbar makudan kudade daga hannun irin wadannan matasa, bisa alkawarin sama masu aikin.
Wani lokaci dillalan kan yi nasarar sama wa matasan aiki bayan kulla cuwa-cuwa a tsakaninsu da wasu jami’ai da ke kula da daukar sababbin ma’aikata a matakin gwamnati a matakin jihohi ko tarayya. Amma a wasu lokuta kuma sukan yi batar kakatantan.
Dillalan aikin gwamnati ‘sun wanke’ ni
Wata matashiya mai shekaru 35 da ta bukaci a sakaya sunanta ta bayyana wa Aminiya yadda ta tashi ba ta ga tsuntsu ba ta ga tarko bayan ta fada a hannun masu damfarar masu neman aiki bayan ta kammala karatu.
Ta bayyana cewa, “Na yi gwanjon wasu kadarorin da na yi gado daga mahaifina wajen biyan kudin karatun jami’an, inda na samu digiri a fannin Ilmin Lafiyar Dabbobi, amma na ci karo da matsalar samun aiki.”
Ta ce daga baya, “Na samu labarin wadannan dillalan bogi da mahaifiyata ta amince da mu sake gwanjatar da kadarorinmu domin biyan su kudi Naira miliyan daya da dubu dari baiyar da suka nema daga gare ni da alkawarin sama min aikin gwamnati.”
A karshen bayanin da hawaye ke zuba a fuskarta cewa ta yi, “Bayan na kammala biyan kudin baki daya sai na daina ganin su a wurin da muka saba haduwa, wanda a karshe na shiga matsananciyar damuwa da ba zan taba mantawa da ita ba domin sun yi layar zana ban san inda zan gano su ba.”
‘Akwai hadin bakin jami’an gwamnati’
Wani tsohon ma’aikacin gwamnati da aka sakaya sunansa, ya ce “Son zuciya da dogon buri daga bangaren manyan ma’aikatan gwamnati ne yake haifar da irin wannan cuwacuwar cefanar da guraben aiki ga daliban da suka kammala karatu.
“Za ka ga cewa da zarar an samu gurbin daukar sababbin ma’aikata sai Babban Sakatare a wannan ma’aikata ya tura ’yan korensa daga cikin kananan jami’an da suke aiki a karkashinsa su fara tuntubar dillalan bogi suna bibiyar dalibai da suke karbar dimbin kudade a hannunsu da suke yin kashe-mu-raba a tsakanin su.”
Ma’aikatu da hukumomin gwamnati sun sha gargadin masu neman aiki da su guji bi ta bayan fage ko abin da zai jefa su a hannun ’yan damfara, musamman a lokacin da cibiyoyin gwamnatin suka sanar da shirin daukar ma’aikata ko aka fara jitajitar hakan.
Hukumomin yaki da ayyukan danfara da dangoginsu sun sha kamawa tare da hukunta irin masu wannan aiki, wani lokaci, hukumomin da abin ya shafa sukan kama tare da hukunta jami’an da abin ya shafa, amma har yanzu ana samun masu kunnen kashi, kuma masu neman aiki ba su daina fadawa a tarkonsu ba.
A kan yadda a wasu lokuta ake kama irin wadannan mutane ba tare da hukunta su ba, sai tsohon ma’aikacin ya ce “tun farko na gaya maka cewa daga sama suke samun daurin gindi daga bangaren manyan ma’aikata.
Abin da ke jefa matasa a tarkon ’yan damfara
Wani mai fashin baki da ke zaune a birnin Akure, Kwamared Ibrahim Shu’aibu, ya ce “Wannan lamari ya zama abin kunya da tausayi da bakin ciki har da mamaki inda mahukunta Nijeriya suke kallon irin barnar da ake yi, wacce ta zama ruwan dare ba tare da daukar matakin shawo kanta ba.”
Kwamared Ibrahim Shu’aibu ya danganta yadda matasa ke fadawa a hannun irin wadannan bata-gari da gaggawa da neman cin bulus. Ya ce, “Mafi yawanci sun taso ne ba tare da koyon kananan ayyuka da sana’o’in dogaro da kai, lamarin da ya taimaka wajen kashe guiwar dalibai, musamman ’yan Arewa da suka fi mayar da hankali wajen dogaro da samun aikin gwamnatoci domin cin banza a maimakon rungumar kananan ayyuka da sana’o’i da kasuwanci da zai taimaka masu dogaro da kansu kamar yadda dalibai a sashen Kudancin kasa suke yi.
Ya ce, “Irin wannan lamari ya zama ihu bayan hari ga Arewa. Gwamnatocin baya sun samu damar hana ci gaba da aukuwar irin wannan barna a zamaninsu sai dai sun yi sako-sako da suka bari lamarin ya ci gaba har zuwa wannan zamani da ’yan siyasa suka kara dagula al’amura.
Mai fashin bakin ya ce “wani abun takaici shi ne yadda za ka ga matasan da suka kammala karatu na da jarin sama da naira dubu 200 a hannunsu amma sun kasa shiga kananan kasuwanci su juya wannan kudin, sun fi so su yi amfani da wannan kudi wajen neman aikin gwamnati da yunkurin fita zuwa kasashen Turai.”
Yadda za magance matsalar
Kwamared Ibrahim ya ce, “muhimmin abun da zai taimaka wajen samun saukin irin wannan tabargaza a tsakanin matasa masu neman aikin gwamnati da dillalan bogi masu karbar miliyoyin kudi daga hannunsu shi ne gwamnatin kasa ta tabbatar da samar da guraben aiki da yin adalci ga miliyoyin matasa domin akwai arzikin da za a iya daukar wannan nauyi.
“Su kuma masu rike da madafun iko su sanya tsoron Allah a kan abun da suke yi wanda yake kara kyamar juna a tsakanin ’yan Najeriya.
“Kuma a tabbatar da hukumta dukkan mai karba da mai bayarwa a domin dukkan su suna da laifi,” in ji shi.