Wasu da ake zargin fusatattun masu faskwaurin shinkafa ne sun kai hari kan jami’an Hukumar Kwastam da ke aiki a shiyyar Yauri ta Jihar Kebbi.
Wannan na ƙunshe cikin wata takarda da kakakin Kwastam shiyyar Yauri, Mohammed Tajudeen Salisu ya aika wa shugaban hukumar a Jihar, Iheanacho Ernest Ojike.
Ya bayyana cewa wasu da ake zargin fusatattun masu shigo da shinkafa ta barauniyar hanya sun kai hari ofishinsu da ke Yauri, inda suka ƙwaci bindiga kirar AK47 guda ɗaya, da buhunan shinkafa 29 daga cikin buhuna 41 da hukumar ta kwace.
Sai dai Salisu ya bayyana cewa bayan artabu da aka yi tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun yi nasarar ƙwato bindigar da maharan suka kwace, amma fa dai shinkafa ta tafi.
- NAHCON ta mayar da kuɗin Hajjin bana kusan Naira miliyan 7
- Gwamnan Kano ya yi ƙarin haske kan kuɗin da zai kashe a rabon abincin azumi
Ya ce, sun samu bayanan sirri da suka nuna cewa akwai masu fasakaurin shinkafa a gaɓar tekun Yauri “ko da isar mu sai muka kama buhunan shinkafa ‘yar waje 41 muka kai ofishinmu.
“To bayan nan ne fusatattun masu shigo da shinkafar suka gayyato ’yan daba, suka far mana a ofishinmu, suka yi nasarar kwashe buhuna 29 daga cikin 41 da muka karbo.
“Sun kwaci bindiga kirar AK47 guda ɗaya, amma mun ƙwato kayarmu bayan artabu da aka sha.”
Ya kara da cewa, maharan sun farfasa motar ofishin, sun lalata na’urar sanyaya wuri da kofofi da tagogi da kujeru da sauran kayayyakin aiki a ofishin na Kwastam da ke Yauri.