✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lakurawa sun kashe mutum 13 a ƙauyukan Kebbi

Harin na ramuwar gayya na zuwa ne bayan wani farmaki da jami’an tsaro suka kai wanda ya yi ajalin wani shugaban ’yan ta’addar da ake…

Mayaƙan Lakurawa sun kashe mutum 13 a wani harin ramuwar gayya da suka kai yankin Birnin Debe da ke Ƙaramar Hukumar Arewa a Jihar Kebbi.

Wani mazauni mai suna Musa Gado, ya ce maharan wanda suka kai harin a ranar Lahadi, sun kuma ƙone ƙauyuka takwas daga cikin tara da ke yankin.

Shi ma wani mazaunin yankin, Suleiman Abubakar wanda ya rasa ɗan uwansa ɗaya a dalilin harin, ya ce maharan sun auka wa ƙauyukan ne da yammaci bayan sallar Magariba.

“Abin ba a cewa komai domin mun ga tashin hankali. Sun kashe mutane da dama sun ƙone mana ƙauyuka kuma babu wanda suka ƙyale hatta mata da ƙananan yara.”

Aminiya ta ruwaito cewa, galibin waɗanda suka jikkata a dalilin harin yanzu haka suna samun kulawa a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Birnin Kebbi.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Arewa, Sani Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamari da cewa tuni an tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin yayin da gwamnatin ke ci gaba da ɗaukar mataki a kan lamarin.

Harin wanda ake zargin na ramuwar gayya ne na zuwa ne bayan wani farmakin haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da gwamnatin Kebbi, wanda ya yi sanadin mutuwar wani shugaban ’yan ta’addar Lakurawa da ake kira Maigemu.

Majiyoyin leƙen asiri sun tabbatar da cewa an kashe Maigemu a yankin Kuncin Baba da ke Arewacin jihar, bayan fafatawar da aka yi a ranar Alhamis ta makon jiya.

Da take martani, rundunar ’yan sandan jihar, ta ce mayaƙan Lakurawa ne suka kai harin a yankunan Birnin Debi, Dogon Daji, Danmarke, Yar Goru, Tambo, Garin Nagoro da kuma Garin Rugga da ke Arewacin jihar.

Rundunar ta ce mayaƙan ɗauke da muggan makamai sun kai hari a waɗannan yankunan da ke iyaka da Jamhuriyyar Nijar, inda suka kashe aƙalla mutum 11 yayin da wasu biyu suka jikkata.

Wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Nafiu Abubakar ya fitar ta ce maharan sun koma ƙone wasu gida ƙurmus a ƙauyukan da abin ya shafa.

Ana iya tuna cewa, a watan jiya na Fabarairu ne wasu ’yan ta’addan suka kashe wani mutum tare da jikkatar wasu shida a yayin harin da aka kai ƙauyen Gulman da ke Ƙaramar Hukumar Argungu ta Jihar Kebbi.

Kazalika, mayaƙan ake ɗora wa alhakin kashe wasu jami’an hukumar shige da fice biyu da wani farar hula ɗaya a Ƙaramar Hukumar Kangiwa.