Wasu ’yan bindiga da ake fargabar mayaƙan Lakurawa ne sun kashe wasu ’yan bijilanti da ke aikin sintiri a Jihar Sakkwato.
Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata bayan musayar wuta da mayaƙan suka yi da ’yan sintiri a Ƙaramar Hukumar Tangaza a jihar ta Sakkwato.
Bayanai sun ce kawo yanzu akwai ragowar gawawwakin ’yan bijilantin da ke hannun Lakurawan a dajin da suka yi sansani.
Sai dai wakilinmu ya ruwaito cewa rundunar soji na ƙoƙarin ƙwato gawawwakin a dajin Binji da Raka.
Shaidu sun ce tun da farko lamarin ya faru ne yayin da ’yan sintirin suka yi ƙoƙarin hana ’yan bindigar shiga ƙauyen Magonho domin kai hari.
Wannan ce ta sanya aka soma musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu, lamarin da ya kai ga salwantar rayukan ’yan bijilantin.
Rahotanni na cewa ’yan bindigar aƙalla 40 haye a kan babura 20 ne suka kai harin da nufin satar dabbobi kafin a ci ƙarfinsu su tsre.
“Sun kashe mana mutane 11 sun kwashi wasu gawar namu sun tafi da su domin wulaƙanci, zuwa yanzu ba za a ce ga yawan mutanen da suka tafi da su.”
Sai dai sojojin da suka yi sansani a yankin sun kawo ɗauki, inda suka yi nasarar ƙwato wasu dabbobni hannunsu.
Kazalika, daga bisani ’yan bindigar sun koma ƙauyen Magonho inda suka tarwatsa turakun sadarwa na kamfanin MTN.
Aminiya ta yi ƙoƙarin jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato, DSP Rufa’i Ahmad, amma lamarin ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton