✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lakurawa sun kashe ’yan sa-kai 13 a Kebbi

Lamarin ya faru ne a ɗaya daga cikin yankunan da ake cewa mayaƙan Lakurawa na da sansani.

Ana fargabar cewa kimanin ’yan sa-kai 13 ne suka rasa rayukansu a wasu hare-hare da wasu ’yan bindiga da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne suka kai Jihar Kebbi a jiya Lahadi.

Lamarin ya faru ne a yankin Morai na Ƙaramar Hukumar Augie — ɗaya daga cikin yankunan da ake cewa mayaƙan Lakurawa na da sansani.

Wani mazauni, Malam Ibrahim Augue, ya ce maharan sun kashe mutum shida ne, suka kwashe shanu, sai ’yan sa-kai suka bi su.

“A nan suka yi wa ’yan sa-kan kwanton ɓauna, suka buɗe musu wuta, inda suka kashe guda 13 daga cikinsu.”

Ƙoƙarin da Aminiya ta yi domin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi, CSP Nafiu Abubakar ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.