✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a tsagaita wuta ta kwanaki 7 a rikicin Sudan

Akalla fararen hula dubu dari biyar rikicin ya daidaita.

Shugabannin bangarorin da suke fada da juna a Sudan sun amince da tsagaita wuta ta tsawon kwanaki bakwai.

Tsagaita wutar da aka kulla a baya dai ba ta yi cikakkiyar nasara ba.

Akalla fararen hula dubu dari biyar rikicin ya daidaita a tsakanin kwanaki 17 da aka kwashe ana gwabza fada a tsakanin Sojin sudan da dakarun RSF.

BBC ya ruwaito cewa, sabuwar yarjejeniyar tsagaita wutar za ta fara aiki ranar Alhamis.

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Sudan ta Kudu ta fitar ta bayyana cewar bangarorin biyu masu rikici da juna sun amince su sanar da wadanda za su wakilce su a tattaunawar sulhu.

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta bayyana aniyar shiga tsakani don sasanta rikicin na Sudan, kuma tuni aka zabe ta a matsayin guda daga cikin kasashen da za su jagoranci sulhun.