✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a rusa gidajen shakatawa 2 a Abuja saboda karya dokokin COVID-19

A karshen mako ne dai aka rufe gidajen shakatawa na Cool Leo da na Paris saboda karya dokokin COVID-19.

Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja (FCTA) ta sha alwashin rusa wasu gidajen shakatawa guda biyu a yankin Karu na Karamar Hukumar Birnin Abuja saboda karya matakan kariya daga COVID-19.

A karshen mako ne dai aka rufe gidajen shakatawa na Cool Leo da na Paris saboda karya dokokin da kuma mayar da gida zuwa wurin kasuwanci.

Shugaban Sashen Wayar da Kan Jama’a na Kwamitin Kar-ta-kwana kan yaki da cutar a Abuja, Ikharo Attah ne ya sanar da hakan a dandalin taro na Eagle Square yayin gurfanar da mutane 29 da aka kama a fadin birnin saboda karya dokokin.

Attah ya ce hukumomi za su ci gaba da fadi tashin ganin babu abinda ya hana su rusa wuraren shakatawar biyu, matukar ba su koma amfani da wuraren kamar yadda aka amince ba.

Ya kara da cewa, “Mun umarci wasu gidajen shakatawa na Paris Club da Cool Leo su rufe. Suna amfani da gidan zama wajen takura wa makwabtansu, lamarin da ya sabawa dokar mu. Mun rufe su har illa ma sha Allahu.

“Idan kuma suka ki amincewa su mayar da shi gida kamar yadda yake a tsari, za mu yi amfani da tsarin birnin Abuja mu rusa su. Ba za mu amince su ci gaba da takurawa jama’a ba.”