Hukumar Gudanarwar Birnin Tarayya za ta rufe Kasuwar Wuse da ke Abuja a ranar Talata saboda saba dokokin takaita yaduwar cutar COVID-19.
Jami’in Wayar da Kan Jama’a na Kwamitin Yaki da COVID-19 da Ministan Abuja ya kafa, Iharo Attah, ya ce kwamitin zai kuma rufe Cibiyar Cinikayya UTC da kuma Morg Plaza dakkanninsu a yankin Area 10 a Abuja.
- An cafke ’yan Kano masu sayar da hotunan mata na batsa
- Dogo Gide: Mutumin da ya hallaka Buharin Daji
- Yadda wakar Hausa ta Sambisa ta tayar da kura
- Tun asali na yi makwabtaka da Sambisa —Yamu Baba
Ya bayyana haka ne bayan Mai Shari’a Idayat Akanni ta yanke hukunci tare da bayar da umarnin a zaman Koutun Majistaren ta tafi-da-gidanka a ranar Litinin.
Jami’in ya ce hukuncin kotun ya zo daidai da dokar da Shugaban Buhari ya sanya wa hannu kan hukunta masu karya dokar cutar.
An kuma gurfanar da kusan mutum 100 a gaban kotun saboda karya dokokokin hana yaduwar cutar COVID-19, musamman rashin sanya takunkumi.