✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a rataye matashin da ya kashe mahaifinsa saboda zargin maita

Matashin ya amince cewa shine ya hallaka mahaifin nasa saboda zarginsa da maita

Babbar Kotun Jihar Akwa Ibom da ke zamanta a Karamar Hukumar Ikot Ekpene ta jihar ta yanke wa wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe mahaifinsa.

An dai yankewa matashin mai suna Edidiong Ototi mai kimanin shekaru 31 a duniya dan asalin Karamar Hukumar Obota Akara hukuncin saboda kisan mahaifin nashi, Pius Ototi wanda ya zarga da maita.

Da yake bayar da jawabi ga ‘yan sanda, matashin ya amince cewa shine ya hallaka mahaifin nasa sannan ya binne shi a cikin masai ranar 18 ga watan Nuwamban 2018.

Da ya ke yanke hukunci a ranar Litinin, alkalin kotun, Mai Shari’a Augustine Odokwo ya ce “Hukuncin laifin da wanda ake zargin ya aikata dogaro da sashe na 326 (1) na Kundin Manyan Laifuka na jihar Akwa Ibom na 2000 shine kisa”.

Akalin ya ce za a rataye matashin ne a wuya har sai ya mutu.

Yanke hukuncin ya biyo bayan gabatar da kwarara kuma gamsassun hujjoji da masu shigar da kara na Ma’aikatar Shari’ar jihar suka gabatarwa kotun.

A cewar alkalin, Edidiong ba shi da damar kashe mahaifin nasa mai kimanin shekaru 60, wanda ya alakanta da kisan jikokinsa guda biyu saboda zargin maitar.

Kafin a kai ga yanke masa hukuncin dai, matashin ya rikide zuwa mai wa’azi a gaban kotu inda ya rika jawo ayoyin Baibul yana rokon alkalin ya yi masa afuwa.