✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a nada sabon Sarkin Yakin Katsina

Sanarwar da Masarautar ta fitar ta ce za'a yi bikin nadin nan gaba.

Majalisar masarautar Katsina ta amince da nada sallaman Katsina kuma Sakataren masarautar Alhaji Bello Mamman Ifo a matsayin sabon Sarkin yakin Katsina.

Ba shi wannan mukami ya biyo bayan rasuwar yayan shi, Alhaji Bishir Mamman Ifo wanda Allah ya yi wa cikawa a satin da ya gabata a kasar Togo bayan wata rashin lafiya.

Kafin rasuwarsa, Alhaji Bishir Mamman Ifo shi ne shugaban Bankin Kasashen Afrika wadda ke da hedkwata a Lome ta kasar Togo.

Shi dai sabon sarkin yakin, kafin ba shi wannan mukami na yayan sa wanda suka gada daga mahaifin su marigayi Alhaji Mamman Ifo, shi ne sallama kuma sakataren masarautar ta Katsina.

Sanarwar da Masarautar ta fitar ta ce za’a yi bikin nadin nan gaba.