Gwamna Aminu Bello Masari a ranar Juma’a ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince a kashe kudi har N6.25bn wajen samar da wuraren kiwo na zamani a Jihar Katsina.
Ya ce da wannan amincewar, yanzu Jihar ce za ta kasance a kan gaba wajen samar da wuraren kiwo a kasar nan.
- Kotu ta aike da Sheikh Abduljabbar gidan yari
- An yanke wa ’yan sanda 2 da wasu mutum 3 hukuncin kisa a Akwa Ibom
Masari, a cewar wata sanarwar da Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu, ya bayyana hakan ne a wajen bikin kaddamar da madatsar ruwa ta Zobe wanda aka kammala bayan shekara 29 da farawa.
Gwamnan ya yaba wa Shugaban bisa kirkirowa tare da aiwatar da ayyukan da mutane za su amfana da su ta hanyar fitar da N5bn domin Jihar ta fara samar da wuraren.
“Mai girma Shugaban Kasa ya amince mana N6.25bn domin samar da wuraren kiwo na zamani a Jihar Katsina.
“Tuni wani bangare na wannan kudin, wato Naira biliyan biyar ya shiga lalitar gwamnatin Katsina, kuma nan da ’yan makonni masu zuwa za ku ga tallace-tallace ana neman kamfanoni masu sha’awar aikin gina wuraren,” inji Gwamnan.
Masari ya ce Gwamnatin Tarayya ta damu matuka wajen inganta rayuwar mazauna karkara, inda ya ce aikin madatsar ruwan na Zobe wani hadin gwiwa ne na samar da sama da lita miliyan 50 na ruwa ga al’ummomin yankin a kullum.
Gwamnan ya kuma gode wa Shugaban Kasar saboda kaddamar da aikin madatsar ruwan da ma aikin hanya mai tsawon kilomita 50 wanda ya tashi daga Dutsin-ma zuwa Taskiya a Jihar.