✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a karrama tsofaffin ’yan kwallon Stationery Stores

Gwamnatin Jihar Legas za ta karrama tsofaffin ’yan wasan kungiyar kwallon kafar jihar mai suna Stationery Stores saboda kwazon da suka nuna a lokacin da…

Gwamnatin Jihar Legas za ta karrama tsofaffin ’yan wasan kungiyar kwallon kafar jihar mai suna Stationery Stores saboda kwazon da suka nuna a lokacin da suka yi wa kulob din wasa.

Wadanda za a karrama suna hada da tsohon kyaftin din kulob din wanda yake fama da rashin lafiya mai suna Yomi Peters da Pa Herbert Omohkaye da George Hassan da Peter Fregene da Kadiri Ikhana da Henry Ogboe da Festus Okubule da Jonathan Nwaiwu da Peter Anieke.
Sauran sun hada da Ayo Ositelu da Aloysis Atuegbu da Ogidi Ibeabuchi da kuma Sunday Dankaro
Kwamishinan wasanni na jihar Enitan Oshodi ya bayyana cewa za a gudanar da bikin karramawar ne a ranar 23 ga wannan wata a filin wasa na Teslim Balogun da ke unguwar Surulere a Jihar Legas.
Oshodi ya ce za a yi bikin ne daidai lokacin da za gudanar da wasa na karshe na kofin kalubale na kasa da za a yi a jihar.
Ya bayyana cewa Jihar Legas ta kammala shirinta tsaf don karbar bakuncin karawar karshe na cin kofin kalubale na kasa.
Kuma a cewarsa karbar bakuncin wasan da jihar za ta yi wani mataki ne na irin yadda gwamnan Jihar Babatunde Raji Fashola yake kokarin dawo da martabar wasanni a jihar.