✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Palermo ta ɗauki Filippo Inzaghi

Palermo ta biya Pisa kusan dala miliyan 1.1 wajen ɗaukar Inzaghi.

Ƙungiyar Palermo ta ɗauki Filippo Inzaghi a matsayin mai horas da ’yan wasanta bayan raba da gari da ƙungiyar Pisa wadda ya kafa tarihin jagorantar haurowarta gasar Serie A.

Cikin wata sanarwa da Palermo ta fitar ta ce Inzaghi ya rattaba hannu kan kwantaragin shekaru da dama wanda zai soma aiki daga watan gobe.

A cewar kafofin watsa labarai na Italiya, Palermo ta biya Pisa kusan dala miliyan 1.1 wajen ɗaukar Inzaghi.

Pisa dai ta ƙare gasar Serie B a mataki na biyu a ƙarƙashin jagorancin kociyan mai shekaru 51, lamarin da ya ba ta nasarar haurowa gasar Serie A karon farko a cikin shekaru 34.

Pisa ta samu gurbi a gasar Serie A bayan samun nasara a wasannin sharar fage da ta buga da Cremonese da kum Sassuolo.

Sabuwar ƙungiyar Inzaghi wato Palermo ta dai ƙare ne a mataki na takwas, kuma ta sha ƙasa a zagayen farko na wasannin sharar fage a hannun Juve Stabia.

AFP