Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta raba gari da mai horas da ’yan wasanta, Thiago Motta, yayin da ko kaka ɗaya bai cika ba a kwantaragin da ya ƙulla da ƙungiyar ta Italiya.
A cewar Jaridar wasanni ta La Gazzetta dello da Gidan Talabijin na Sky Sport, Juventus ta maye gurbin Thiago Motta da tsohon ɗan wasan ƙungiyar, Igor Tudor.
Juventus dai za ta ɗora wa sabon kocin nauyin jajircewa wajen ganin ƙungiyar ta ƙare a cikin sahun huɗun farko na teburin Gasar Serie A ta bana, domin samun damar buga Gasar Zakarun Turai a kaka mai zuwa.
A halin yanzu ƙungiyar da ke fama da rashin kuɗi, ita ce ta biyar a teburin Serie A yayin da ya rage sauran wasanni 9 a ƙarƙare gasar.
Kafofin watsa labarai daga Italiya sun ruwaito cewa nan da kowane lokaci ƙungiyar za ta fitar da sanarwa a hukumance ta raba gari da Thiago Motta mai shekaru 42 da kuma naɗa magajinsa, Igor Tudor.
A watan Yulin bara ne dai Thiago Motta ya karɓi ragamar jagorancin ƙungiyar bayan ya yi ƙoƙari matuƙa a ƙungiyar Bologna a kakar 2023/24.
Sai dai a yanzu duk gwiwowinsa sun yi sanyi sakamakon rashin kataɓus a ƙungiyar da ake yi wa laƙabi da Old Lady.
A ƙarƙashin jagorancin kociyan ɗan ƙasar Brazil, Juventus ta buga wasanni 42, inda ta yi nasara a 18 da canjaras 16 sai kuma rashin nasara a wasanni takwas.
A watan Fabrairun da ya gabata ne ƙungiyar PSV ta koro Juventus daga Gasar Zakarun Turai, sannan Empoli ta fatattako ta daga Kofin Italiya.
Wasanni biyu na bayan nan da Motta ya jagorancin ƙungiyar ta gamu da rashin nasara a hannun Atalanta wadda ta lallasa ta da ci 4-0 — wadda ita ce rashin nasara mafi girma da ta yi a gida tun 1967 — sai kuma kashi da ta sha a hannun Fiorentina da ci 3-0.