✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Najeriya ya zama dan Afirka na farko da ya lashe kyautar takalmin zinare a Italiya

Karo na farko ke nan da Napoli ta lashe gasar Serie A cikin shekaru 33.

Dan wasan Najeriya da Napoli, Victor Osimhen ya lashe kyautar takalmin zinare a Italiya, bayan da ya zama dan wasan da ya ci mafi yawan kwallaye a gasar Serie A.

Nasarar dai ta ba shi damar kafa tarihin zama dan Afirka na farko da ya kai wannan mataki.

Karin tarihin da Osimhen ya kafa kuma shi ne zama dan wasa na farko da ya samu nasarar hade kyautar takalmin zinare da kuma lashe kofin gasar Serie A a lokaci guda, da ake kira da ‘Scudetto’ tun shekarar 2009, lokacin da Zlatan Ibrahimovic ya kafa nasa tarihin a kungiyar Inter Milan.

Kwallaye 25 Osimhen ya ci a kakar wasa ta bana, yayin da mai biye da shi Lautaro Martinez na Inter Milan ke da kwalllaye 21.

A halin yanzu Osimhen ne dan wasan Napoli na hudu da ya lashe kofin gasar Serie A da kuma kyautar cin mafi yawan kwallaye, inda ya bi sahun Diego Maradona, Edison Cavani, da Gonzalo Higuain.

Karo na farko ke nan da Napoli ta lashe gasar Serie A cikin shekaru 33.

A makonnin bayan nan ne dai Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa ta Napoli, Aurelio De Laurentiis, ya ce ba zai sayar da Victor Osimhen ba a cikin kasuwar bazarar nan ta musayar ’yan wasa.

Aurelio ya yi wannan furuci ne a daidai lokacin da manyan kungiyoyi irinsu Bayern Munich da PSG da Manchester United da Chelsea da Arsenal ke rububin sayo dan wasan na Najeriya.

Yanzu haka shugaban na Napoli ya ce, yana da shirin ci gaba da rike zaratan ’yan wasansa har zuwa kaka mai zuwa kuma zai tsawaita kwantiragin kocin kungiyar Luciano Spalletti kamar yadda ya fadi.