✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burna Boy ya kafa tarihin sayar da tikitin filin wasa

An sayar da tikiti na filin wasan kaf!

Fitaccen mawakin Najeriya, Damini Ebunoluwa Ogulu, wanda aka fi sani da Burna Boy, ya kafa tarihin zama mawakin Afirka na farko da ya sayar da tikitin filin wasa na Landan mai daukan mutum 80,000.

Filin wasan na kungiyar kwallon kafa ta West Ham ne da ke Landan.

Hukumar da ke kula da filin wasan na Landan ce ta sanar da hakan a shafinta na Twitter.

A ranar 3 ga watan nan na Yuni Burna ya yi wasansa na kade-kade a filin wasan, wani bangare na rangadin da yake yi, wanda ya yi wa take da “Burna Boy’s Love, Damini Tour.”

Yayin wasan wanda aka yi a ranar Asabar, Burna Boy ya kayatar da masoyansa da fitattun wakokinsa.

“SOLD OUT wato an sayar da tikiti na filin wasan kaf!! @burnaboy’s RECORD-BREAKING concert, yanzu an sayar da shi gaba da ya a hukumance!

“Wannan babbar nasara ce ga dan wasan Afirka na farko da ya taba tsayawa gwarzo tilo a filin wasa na Birtaniya!” Hukumar filin wasan ta ce.

Wasan ya kuma ya hada da wasu manyan mawaka na duniya irin su Stormzy, Popcaan, da Dave & Jhus wadanda suka taya wannan jarumin na Afirka wajen baiwa dubban masoya kade-kade jin dadi a daren.

Magoya bayansa sun rufa mishi baya suna ta rera waka a duk lokacin da Burna Boy ya ke waka, ya yi wakoki sama da 40.

Daga karshe Burna Boy ya ce “Na gode London da Soyayya da kaunar da kuka nuna min da kuma duk wanda ya goyi bayana wajen kafa tarihi!! Sai mun sake haduwa.”

Bayan an kammala wasan wake-waken, an ba Burna Boy lambar yabo da girmamawa.