✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a kara kudin burodi a Kano

Nan gaba kadan za a sanar da sabon farashin burodi a Kano.

Kungiyar masu gidajen burodi a Jihar Kano ta ce watakila nan gaba burodi zai kara kudi saboda tsadar da fulawa ta yi, wacce ita ce jigo a hada burodin.

A ranar Juma’a kungiyar kwararru masu gasa burodi da girke-girke ta kasa reshen jihar ta sanar da cewa lura da tsadar fulawar, yanzu ba ta da wani zabi illa ta kara kudin burodin, ta haka ne kadai za su ci gaba da gudanar da sana’ar tasu.

Matakin na zuwa ne kwanaki kadan bayan da masu gasa gurasa, wacce ta kasance mai kamshin dan goma a wajen Kanawa, suka yi barazanar shiga yajin aikin sai abin da hali ya i sakamakon tsadar da fulawar ta yi – da ta kasance ginshiki wajen yin gurasar.

Da yake magana da manema labarai a Kano ranar Juma’a, Sakataren kungiyar masu gasa burodin, Kabiru Hassan Abdullahi, ya ce kungiyar ta yanke shawarar kara farashin ne domin tabbatar da dubban matasa ba  su rasa na yi ba idan har suka daina gasa burodin.

Ya yi kira ga gwamnati da ta kawo dauki wajen kawo karshen yawan hauhawar farashin fulawar da sauran kayayyakin masarufi a Najeriya.

Ya ce sau da dama kungiyar tana kokarin zama da masu kamfanonin hada fulawa domin karya farashinta, amma hakarta ba ta cimma ruwa ba.

Sakataren ya nunar da cewa buhun fulawan da a farkon bara ake sayar da shi kan N9,000 yanzu ya koma N16,000 zuwa sama.

A cewarsa, bayan taron da kungiyar ta gudanar ranar Laraba, an umarci mambobinta da su gana da kananan masu gasa burodin da zimmar fito da sabon farashin burodin na bai daya nan da kwana 10.