More Podcasts
Burodi ya zama daya daga cikin abincin da ‘yan Najeriya basa iya yi babu shi. Yayin da wasu ke cin shi a matsayin abin Karin kumallo da safe, wasu kuwa na cin shi a matsayin abincin rana a wasu lokutan ma har da na dare.
A duk lokacin da aka ce masu sarrafa burodi sun shiga yajin aiki, ko fulawa tayi karanci hakan kan haifar da raguwar burodi a kasuwa wadda kan jefa masu cin shi a cikin mawuyacin hali.
- NAJERIYA A YAU: Halin da al’ummar Mokwa ke ciki wata guda bayan ambaliya
- DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi?
Shirin Najeriya A Yau na wannan makon zai yi nazari ne kan sinadaran da ake amfani da su wajen sarrafa burodi da kuma irin cutar da suke jawowa.
Domin sauke shirin, latsa nan