Kungiyar masu gidajen burodi da masu shayarwa ta Najeriya ta sanar da shirinta na shiga yajin aiki a fadin kasar saboda tsadar kayan hada burodi da dangoginsa.
Shugaban AMBCN na jihar Kogi, Adeniyi Bamidele Gabriel ya sanar ranar Talata cewa za su fara yajin aikin ne daga ranar 27 ga watan nan na Fabrairu.
Ya bayyana cewa shugaban kungiyar na kasa Mansur Umar, tare da sakataren kungiyar na kasa, Jude Okafor sun fitar da sanarwar hakan.
A cewarsa, za su shiga yajin aikin ne “saboda hauhawar farashin kayayyakin burodi da man fetur da dizel sakamkon cire tallafi, tashin Dala, rufe boda da kuma haraji mai yawa da muke biyan hukumomin gwamnati”.
- Yadda Yajin Aikin ’Yan A Daidaita Sahu Ya Tsayar Da Harkoki a Yobe
- An kama su suna lalata a coci a hedikwatar ’yan sanda a Borno
AMBCN na cewa gwamnatin tarayya na karbar haraji daban-daban daga gare su, ta hanunu hukumomi irin su NAFDAC, SON, NESREA, da sauransu.
Kungiyar ta kara da cewa jihohi da kananan hukumomi ma na karbar nasu, lamarin da ke dagula harkokin kasuwanci ga kungiyar.
Don haka ta bukaci abubuwa kamar haka domin saukaka harkokin kasuwancinsu:
Ba wa masu higo da masana’antun fulawa canjin dala da sauki, da kuma rage harajin shigo da fulawa da sukari
Haɓaka noma da sarrafa alkama da rake a Najeriya, cire haraji da yawa a matakin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.
Dakatar da karbar duk wani nau’i na haraji na wucin gadi kan masana’antar burodi, a duk matakan gwamnati.
Kuma a kafa kwamitin kula da farashin kayayyaki da abubuwan da za su inganta saukin kasuwanci a kasar.