✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama su suna lalata a coci a hedikwatar ’yan sanda a Borno

An kama wani matashi da budurwarsa a yayin da suke tsaka da jima'i a cikin coci a hedikwatar ’yan sanda da ke Jihar Borno.

An kama wani matashi da budurwarsa a yayin da suke jima’i a cikin coci a hedikwatar ’yan sanda da ke Maiduguri, Jihar Borno.

Faston cocin, Rabaran Danjuma Adamu ya shaida wa Aminiya cewa yana ofishinsa ne aka zo aka sanar da shi cewa ga wasu suna yin jima’i a cikin cocin.

Da ya garzaya cocin aka kama masu matasan, sai aka samu dukkansu Musulmai  ne, kuma nan take ya sanar da yan sanda.

“Wannan abin kunya ne da rashin sanin darajar wurin ibada, amma mun sanar da yan sanda aka kama su aka tsare su a ofishin Metro.

“Ba su musanta cewa jima’i suke yi a cikin cocin ba, lokacin da aka kama su.

“Su da kansu suka yi ikirari don haka yanzu suna tsare da su,” in ji Rabaran Dajuma.

Lamarin ya faru ne a safiyar ranar Litinin a cikin cocin All Saints Protestant, wanda ke Kwalejin ’yan sanda da ke Maiduguri.

Majiyarmu ta yan sandan ta ce budurwar ta amsa cewa matashin ya biya ta kudi Naira 1,000 don yin amfani da ita.

Da wakilinmu ya tuntubi kakakin yan sandan jihar Borno, ASP Nahum Daso Kenneth, kan lamarin, jami’in ya yi alƙawarin bincikawa, amma da wakilin namu ya sake kiran sa, babu amsa, har aka kammala hada wannan rahoto.