✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a jima kafin a samu kyakkyawar hadin kai a kasashen Larabawa – Ministan katar

Ministan Harkokin kasashen wajen katar ya ce zai dauki dogon lokaci kafin a samu hadin kai da yarda a tsakanin kasashen Larabawa saboda matsalar alaka…

Ministan Harkokin kasashen wajen katar ya ce zai dauki dogon lokaci kafin a samu hadin kai da yarda a tsakanin kasashen Larabawa saboda matsalar alaka da ke tsakanin kasashen.

A daidai lokacin da kaurace wa kasar katar da kasashen Labarawa suka yi ya kai mako 11, Ministan Harkokin kasashen wajen Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al-Thani ya ce alakar da ke tsakanin kasashen yankin ya bace saboda rashin jituwar da aka samu. 

“kasar katar na cikin wadanda suka assasa kungiyar GCC, kuma muna tunanin kungiyar na da muhimmanci matuka ga wannan yankin,” inji shi.

Ita kungiyar hadin kan kasashen Labarawar wato GCC an kirkire ta ne a shekarar 1981 a matsayin kungiyar siyasa da tattalin arziki, kuma ta kunshi kasashen Bahrain, Kuwait, Oman, katar, Saudi Arabia da Hadaddiyar Daular Larabawa.

Ya kara da cewa “Wannan kungiyar an kafa ne domin samar da tsaro kuma an kafa ta ne da aminci.

“Amma abin takaici, saboda abin da ya faru a ‘yan kwanakin baya, yanzu an rasa asalin manufar kafa wannan kungiyar, sannan kuma zai dauki dogon lokaci kafin a dawo da shi kamar yadda yake, amma muna fata zai dawo din,” inji ministan harkokin kasashen wajen.

Za a iya tunawa, kasashen Saudi Arabia, Bahrain, Hadaddiyar Daular Larabawa da Misra sun yanke alaka da kasar katar a ranar 5 ga watan Yuni, inda suka zargi kasar da tallafawa ‘yan ta’adda da kuma alaka da kasar Iran, wanda hakan ya zamo sanadiyar babbar rikicin siyasa a yankin kasashen Larabawa da aka dade ba a samu kamar shi ba.

Ita dai kasar katar tuni ta musunta zargin da ake mata, sannan kuma ita ma ta zargi kasashen da nema su mata kushe a cikin daular ta.

Hakanan kuma kasashen sun daina mu’amala da kasar ta katar, kuma suka hana jiragen kasar sauka a filayen jirgin su.

Ministan kasar wajen kasar ya kara da cewa rikicin bai kamata ba

“Ba ma bukatar irin wannan rikicin a yankin kasashen Larabawa. Muna da wasu matsalolin da wasu rikice-rikicen da suka ishe mu.

“Yankin da ya fi kowane yankin zaman lafiya yanzu ya shiga cikin rudu da hatsaniya a kan wani dan karamin dalili da bai da asali.”

Sai dai kuma ya kara da cewa ana ci gaba da yin sulhu wanda kasar Kuwait ke jagoranta.

“Mun samu wata takarda daga Sarkin Kuwait kwanakin baya, kuma takardar na cikin kokarin da kasar ke yin a samar da sulhu a yankin, inda takardar ta bukaci dukkan kasashen su zauna a teburin sulhu,” inji shi.