Shugaban Hukumar Agajin ta Yankin Birnin Tarayya, Alhaji Abbas Idris, ya bayyana barnar da masu fasa dakunan ajiye kayan abinci suka yi a Abuja a matsayin abun da za a jima ba a maye gurbinsa ba.
Abbas ya ce bata-garin sun fake da zanga-zangar #EndSARS sun lalata daukacin abun da aka adana don raba wa mabukata, kuma sun sace har da kayan koyar da sana’o’i da aka tanadar.
- Aisha Buhari ta ja hankalin Iyaye Mata kan muhimmancin kula da lafiya
- ‘Ciyar da daliban Kano kan lakume N4bn duk shekara’
A hirar da Aminiya ta yi da shi kai-tsaye a shafinta na Facebook a Larabar nan, shugaban hukumar na FEMA ya ce, “A nan Abuja mun bi tsari mai kyau wurin rabon kayan inda muka je gida-gida muka raba a lokacin kullen coronavirus.
“Abun da aka gani da sunan kayan tallafi kungiyoyi ne suka kawo mana, muna dab da rabawa washegari aka far wa kayan aka kwashe”.
A amsarsa ga tsokacin masu kallon shafin Aminiya a lokacin tattaunawar, Abbas ya ce hukumarsa na maraba da duk mai son ganin kwakwaf kan tsarin da ta bi wurin rabon kayan, su nuna masa komai daki-daki.
Don ganin yadda ta kaya, za ku iya kallon cikakkiyar hirar a shafinmu na Facebook mai suna aminiyatrust.