✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ’yan bindiga — Sarkin Musulmi

Sarkin ya koka kan yadda hare-haren 'yan bindiga ya gurgunta kasuwanci a yankin.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya ce za a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ‘yan bindiga a Arewa Maso Yammacin Najeriya.

Sultan ya bayyana ne, yayin taron inganta yanayin tsaro da aka gudanar a ranar Litinin a Jihar Katsina.

“Abin da ya kamata mu yi shi ne ƙalubalantar waɗannan ‘yan bindiga saboda mun san irin illar ‘yan tada ƙayar baya ga rayuwarmu. Sai dai za a shafe tsawon shekaru kafin a kawo ƙarshen matsalar gaba daya,” in ji shi.

Ya ce sarakunan gargajiya a shirye suke domin haɗa gwiwa da jami’an tsaro da kuma gwamnonin yankin domin ƙarshen ayyukan ’yan ta’addar.

A yayin taron, Sarkin Musulmi ya koka kan yadda hare-haren ’yan bindiga a yankin suka gurgunta harkokin kasuwaci tare da kawo koma baya ga ci gaban yankin.

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya wakilci shugaba Bola Tinubu, da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, gwamnoni bakwai na jihohi da ke Arewa Maso Yamma, shugabannin hafsoshin tsaro da kuma sufeton ‘yan sanda na ƙasa.