✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Ganduje ya isa Kano domin halartar jana’izar surukarsa

Sakataren yaɗa labaran Ganduje ne ya sanar sa rasuwar surukar tasa a ranar Litinin.

Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya isa Jihar Kano, domin halartar jana’izar surukarsa.

Aminiya ta ruwaito cewar surukar tsohon gwamnan Hajiya Asiya Gauyama, wadda mahaifiya ce ga matarasa Hafsat Abdullahi Ganduje, ta rasu a ranar Litinin.

Babban sakataren yaɗa labaran Ganduje, Edwin Olofu ne, ya sanar da rasuwarta a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Litinin.

Olofu, ya bayyana cewa za a yi jana’izarta a Kano da misalin ƙarfe 2 na rana, kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar.

Ga hotunan yadda shugaban APC ya sauka a Kano: