Majalisar Dinkin Duniya ta ce za a iya fitar da mutum miliyan 100 a fadin duniya daga kangin talauci nan da shekarar 2025.
Majalisar ta ce duk da barazanar koma-bayan tattalin arziki da ake fuskanta, abu ne da zai yiwu a raba mutum miliyan 100 da talauci nan da shekarar 2025.
- Mutum 14 sun rasu, gidaje 50 sun salwanta a ambaliyar Gombe
- Kotu ta yanke mata daurin rai-da-rai kan mutuwar mijinta
Sakamakon binciken da majalisar ta fitar kan taulaci, ya nuna za a iya rage talaucin da ake fama da shi, a kuma samar da sababbin dabaru a fagen yaki da talaucin don taimaka wa gwamnatoci wajen cimma wannan kudiri.
Majalisar ta fitar da sakamakon binciken ne a Ranar Yaki da Talauci ta Duniya, wadda akan yi ran 17 ga Oktoban kowace shekara.
Ta ce, domin cim ma nasara a wannan yaki, tilas ne shugabanni da kasashe su mike tare da daukar ingantattun matakan dakile abubuwan da suke haddasa talauci a cikin al’umma.