Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA), Gianni Infantino ya ce akwai yiwuwar a buga wasu wasannin cin Kofin Duniya a kasar Kuwait a shekarar 2022 da za a yi a kasar Katar.
Infantino ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci Kuwait don kallon wasan karshe na gasar Yariman Kuwait inda ya shaida wa manema labarai cewa, za a iya buga wasu wasannin gasar ta FIFA ta 2022 a Kuwait.
Infantino ya ce, ya yi wuri a kawo batun kara yawan kungiyoyi daga 36 zuwa 48 inda ya ce matukar hakan ta tabbata to za a samu karin mahalarta gasar daga Nahiyar Asiya.
Shugaban na FIFA ya ce ya ji dadi da samun kungiyar kwallon kafa ta mata ta farko a Kuwait kuma ya kamata dukan kasashen yankin su yi koyi da Katar.