Borussia Dortmund ta soma buɗe wasanninta na gasar FIFA Club World Cup da canjaras a karon-battar da ta yi da kungiyar Fluminense ta Brazil a ranar Talata.
Ana dai ganin babbar kungiyar da ta zama gagarabadau a Rio de Janeiro Fluminense a matsayin mafi hatsari a rukunin F wanda ya kunshi har da kungiyar Ulsan HD ta Koriya ta Kudu.
- Buni ya bai wa manoma 1,000 tallafin aikin gona
- Amurka na iya kashe jagoran addini na Iran don mun san inda yake — Trump
An dai rika kai wa juna hari a yayin wasan da suka barje gumi a filin wasa na Metlife da ke East Rutherford a wajen birnin New York, sai dai mai tsaron ragar Dortmund, Gregor Kobel ya ceci kungiyarsa bayan wata kwallo da Jhon Arias ya nano masa daga nesa tun kafin tafiya hutun rabin lokaci.
Fluminense wadda tsohon dan wasan PSG da Chelsea, Thiago Silva mai shekaru 40 shi ne kyaftin dinta, ta yi kokarin samun damar Dortmund ana tsaka da kai ruwa na bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, amma Kobel ya rike kwallon da Agustin Canobbio ya yi yunkurin tarar numfashinsa.
Golan dai ya sake yin wata bajintar bayan ya tare kwallon da Everaldo ya yi sakada masa a kusurwar kasa, lamarin da haka a karkare wasan babu ci.
Fluminense dai ta samu gurbin zuwa gasar Club World Cup ta bana bayan nasarar lashe Copa Libertadores da ta yi a shekarar 2023.
Bajintar da Fluminense ta yi a karon-battar ta da manyan kungiyoyin da suka kasance zakaran gwajin dafi a nahiyyar Turai ya kara tabbatar da cewa tana iya tabuka abin a-zo-a-gani a gasar Club World Cup ta bana da aka sauyawa fasali.
Dortmund za ta yi fatan samun nasara a wasan gaba da za ta fafata da kungiyar Mamelodi Sundowns ta Afirka ta Kudu.
AFP