Borussia Dortmund da Real Madrid za su kece raini a wasan karshe na Zakarun Turai da misalin karfe 8:00 na Yammacin wannan Asabar a filin wasa na Wembley da ke birnin Landan.
Wannan ne karo na 15 da za su fuskanci juna a tsakaninsu, inda haduwarsu ta baya baya ta kasance wadda Real Madrid ta ci Dortmund gida da waje a wasan rukuni na kakar 2017-2018.
- Abin da ya haddasa rushe Kasuwar Alaba Rago — ’Yan Arewa
- Yadda ’yan gudun hijirar Borno ke rayuwar ƙunci a Ibadan
Dortmund ta bayar da mamaki da ta kawo wannan matakin karshen a kakar bana, bayan da ta ja ragamar rukuni na shida a Champions League.
Ita ce ta yi ta daya a rukunin da maki 11, sai PSG ta biyu da maki takwas da AC Milan ta uku da kuma Newcastle United a gurbin da ya fi kowanne zafi.
Haka kuma kungiyar ta Jamus ta fitar da PSV a zagaye na biyu da yin waje da Atletico Madrid a quarter finals da doke PSG gida da waje a daf da karshe.
Real Madrid ce ta ja ragamar rukuni na uku da maki 18 – ta fuskanci kalubale da yawa, musamman a karawa da RB Leipzig da Manchester City da kuma Bayern Munich da ta kai karawar karshe.
Real Madrid, wadda Carlo Ancelotti ke jan ragama ta lashe La Liga na bana na 36 jimilla, kenan za ta so daukar Champions League na 15 a tarihi.
Madrid ta yi wasa 12 ba tare da an doke ta ba a Gasar Zakarun Turai ta kakar nan da yin nasara takwas da canjaras hudu.
Ita kuwa Dortmund ta yi rashin nasara daya daga 11 da ta fafata a Gasar Zakarun Turai da nasara bakwai da canjaras uku da yin wasa shida ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba, kuma ita ce ke fara zura kwallo a raga karo tara daga fafatawa 10.
Wasan karshe a Gasar Zakarun Turai da Dortmund ta buga shi ne a Wembley, inda ta yi rashin nasara 2-1 a hannun Bayern Munich a 2013.
Ita kuwa Real Madrid ta sha fafatawa da kungiyoyin Jamus a wasan karshe, wadda sau daya ta yi rashin nasara a hannun kungiyar Bundesliga daga 20 da cin 13 da canajaras shida a babbar gasar tamaula ta Zakarun Turai.
Real Madrid da Borussia Dortmund sun kara a Gasar Zakarun Turai sau 14 a tsakaninsu, inda Real ta ci wasa shida da canjaras biyar, Dortmund ta ci karawa uku.
Kungiyoyin biyu sun hadu ne a Gasar Zakarun Turai, inda suka fara fuskantar juna ranar 1 ga watan Afirilun 1998, inda Real Madrid ta yi nasarar cin 20.
Wasa na biyu kuwa da aka yi a Jamus ranar 15 ga watan Afirilu, sun tashi ba ci a fafatawar.
To sai dai wannan shi ne karon farko da za su fafata a wasan ƙarshe na Gasar Zakarun Turai.
Real Madrid na fatan lashe gasar jimilla 15 a tarihi, ita kuwa Dortmund za ta yi iya yinta don ganin ta lashe gasar karo na biyu, sai dai masu iya magana na cewa ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare.