Hedikwatar Tsaron Najeriya ta sha alwashin kama masu hada kai da ’yan bindiga tana mai cewa ta kirkiro sabbin dabarun yakar su da magance matsalar tsaro.
Kakakin rundunar, Manjo Janar John Enenche, ya jaddada cewa dakarun rundunar na kara kaimi wajen murkushe masu hada kai da masu aikata laifuka.
- ‘Yan bindiga sun sace mutum 8 a Edo
- ’Yan bindiga sun sace ’yan sanda 12 a hanyar Zamfara-Katsina
- Jiragen yaki sun kashe ’yan bindiga 17 a Katsina
- ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro uku a Kaduna
“Mun samu rahoton ganin wani dan bindiga a kauyen Kukar Samu da ke Karamar Hukumar Safana a Jihar Katsina.
“Mun kuma yi nasarar kama wasu mutum biyu da ke hada baki da ’yan bindigar yayin da suke shirin tserewa a kan babur din ’yan bingidar.
“Sannan mun kama wani mutum a kauyen Muniya wanda ya ce shi manomi ne, amma bayan gudanar da bincike muka gano yana hada baki da ’yan bindiga ne wajen yin garkuwa da mutane”, inji Enenche.
Ya kara da cewa jami’an tsaro sun kashe da yawa daga cikin ’yan bindigar da ke addabar yankunan Jihar Katsina, yayin da wasu suka jikkata wasu kuma suka tsere.
Har wa yau, ya shaida wa manema labarai cewa an kama mutane da dama da suke hada baki da ’yan bindiga wajen yin garkuwa da mutane daga ranar 12 zuwa 18 ga watan Nuwambar 2020.
Jami’in ya ce sojoji sun kama tarin makamai da alburusai a yayin da suka kama ’yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma na kasar nan.