✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a hukunta magoya bayan FC Barcelona saboda yi wa Cristiano Ronaldo ihun ya yi marisa

Hukumar shirya kwallon kafa ta Sifen ta ce ta fara yin bincike akan yiwuwar daukar mataki a kan magoya bayan kulob din FC Barcelona saboda…

Hukumar shirya kwallon kafa ta Sifen ta ce ta fara yin bincike akan yiwuwar daukar mataki a kan magoya bayan kulob din FC Barcelona saboda ihun da suka rika yi a kan dan kwallon Real Madrid Cristiano Ronaldo akan ya yi marisa, a ranar Lahadin da ta wuce a lokacin da kulob din yake buga wasa da na Lebante a gasar La-Liga ta Sifen.

Duk da yake kulob din ba yana wasa da na Madrid a lokacin ba ne, amma wasu daga cikin magoya bayan kulob din su kimanin 200 da ake musu lakabi da Almogabers, sun rika rera wakar “Ronaldo ya yi marisa, ya sha kafso” ne a matsayin zargin da aka yi wa dan kwallon cewa ya sha giya ya yi tatil a lokacin da ya yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa jim kadan bayan kulob din Atletico Madrid ya yi wa na Madrid kaca-kaca da ci 4-0 a wancan mako a gasar La-Liga.
Hakan ta sa aka rika sukar dan kwallon a kan rashin nuna damuwarsa na abin da ya samu kulob din na lallasawar da kulob din Atletico Madrid ya yi musu.
Magoya bayan Real Madrid ma sun nuna bacin ransu a kan labarin tatil da giya da dan kwallon ya yi. Sai dai Ronaldo ya sha nanata cewa ba ya shan giya ko sigari kuma ya karyata zancen da aka baza na cewa ya sha giya a ranar bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Hukumar shirya kwallon kafar ta ce da zarar ta samu magoya bayan da laifin da ake zargin sun aikata, ko shakka babu za ta dauki mataki na cin tarar kulob din FC Barcelona da kuma magoya bayan kulob din don ya zama darasi ga na-baya.