A yayin da gwamnatin jihar Filato ta kafa dokar hana fita a jihar, wadda ta fara aiki a daren ranar Alhamin din nan.
Gwamnatin ta kafa kotunan tafi da gidanka na musamman guda 10, don hukunta duk wadanda suka karya wannan dokar.
A wata sanarwar da ta fito da ke dauke da sanya hannun Kwamishinan watsa labaran jihar Mista Dan Manjang, ce ta bayyana haka.
Sanarwar ta yi bayanin cewa, an kafa wadannan kotuna ne don ganin an tabbatar al’ummar jihar, sun yi biyayya ga wannan doka, da aka kafa da nufin kare yaduwar annobar coronavirus a jihar. Don haka sanarwar ta shawarci al’ummar jihar su yi biyayya da wannan doka, ta hanyar zama a gida.
Tun da farko dai gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta kafa dokar hana fita tare da rufe jihar gabaki ne, don ganin ta kare annobar Kurona shiga cikin jihar, har na tsawon mako guda.
Gwamnatin tayi bayanin cewa, a yayin wannan rufe jihar da aka yi, tare da hana fitar jama’a. Za a yi feshin magungunan kashe cututtuka a garin Jos da kewaye, da dukkan kananan hukumomin jihar 17.
Har’ila yau Gwamnatin ta ce, a yayin wannan zaman gida wadanda za a bari su ci gaba da zirga-zirga su ne jami’an tsaro da ma’aikatan kiwon lafiya da ‘yan jarida da masu gidajen mai da ma’aikatan kashe gobara.