Mutum daya ya rasu wasu akalla 60 na kwance a asibiti bayan bullar cutar Kwalara a Karamar Hukumar Kanam da ke Jihar Filato.
Shugaban karamar hukumar, Ayuba Salihu Musa, ya ce an fara samun bullar cutar ce a unugwannin Ngyang da kwalmiya da Banak da Bakin kogi inda daga bisani ta yadu zuwa Dengi, hedikwatar karamar hukumar.
Ya ce an kwantar da mutum 60 a Babban Asibintin karamar hukumar da kuma cibiyar kula da lafiya a matakin farko da ke Dangi da wasu asibitoci masu zaman kansu.
A cewarsa, hukumar gudanarwar karamar hukumar ta dauki kwararan matakan dakile yaduwar cutar ta hanyar samar da magunguna da raba su ga asibitoci sannan ta biya kudin maganin marasa lafiyan.
- Mutum 25 sun rasu bayan bullar sabuwar Annoba a Sakkwato
- Lakurawa: Yadda sojoji ke aikin murkushe ’yan ta’adda
Hakazalika ta dauki matakin wayar da kan jama’a kan matakan kariya domin hada bazuwar cutar, wadda ake kamuwa da ita a sakamakon rashin tafstar abinci ko na muhalli.