✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wutar Lantarki ta dawo a Arewa

An shafe aƙalla kwanaki 10 babu wutar lantarki a jihohin Arewacin Nijeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa wutar lantarki da a bayan nan ta yi nisan kiwo ta dawo a wasu jihohin Arewacin Nijeriya.

Aminiya ta ruwaito cewa, an samu wutar lantarkin da yammacin wannan Larabar a jihohin Filato da Bauchi da Gombe da kuma Benuwe.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, mazauna birnin Jos da ke Jihar Filato sun shiga sowa da farin cikin bayan dawo da wutar lantarkin da misalin ƙarfe 7:20 na yammacin wannan Larabar.

Bayanai sun ce an shafe aƙalla kwanaki 10 babu wutar lantarki a jihohin Arewa da dama, lamarin da ya tsayar da harkokin kasuwanci bayan katsewar tashar samar da wutar lantarki da ke jihohin Benuwe da Enugu.