Akalla matasa 13 ne ake fargabar sun mutu bayan ruftawar kasa a wurin hakar ma’adinai a Karamar Hukumar Bassa da ke Jihar Filato.
Aminiya ta lura cewa yawancin masu hakar ma’adinan da suka rasu matasa ne masu shekaru 18 zuwa 30.
Shugaban karamar hukumar, Dokta Joshua Riti, ya ce mutum bakwai daga cikin mamatan ’yan asalin karamar hukumar ne.
Ya bayana cewa wurin hakar ma’adinan da abin ya faru, ya yana kan iyakan kananan hukumomin Bassa, Jos ta Kudu da kuma Jos ta Arewa.
- ’Yan ta’adda sun kona gonaki 6 kafin a girbe abincin da aka noma a Kaduna
- Lakurawa na amfani da jirgi mara matuki, sun karɓe iko a kauyukan Kebbi —Bukarti
“Wannan abin takaici ne, matasa suna neman abin dogaro da kansu irin wannn ya rutsa da su.
“Sun fita suna aikin karfi domin rufa wa kansu asiri a wannan lokaci da ake fama da matsin tattalin arziki, amma suka gamu da ajalins,” in ji Dokta Riti.
Daga nan ya mika ta’aziyyarsa ga iyalai da abokan arzikin da abin ya ritsa da su.