’Yan bindiga sun kashe mutane arba’in a wani hari suka kai a ƙauyukan Zike da Kimakpa, a yankin Kwall da ke Ƙaramar Hukumar Bassa a Jihar Filato.
Wani shugaban al’ummar Kwall, Wakili Tongwe, ya ce maharan sun shiga ƙauyen ne da sanyin safiyar ranar Litinin suna harbi kan mai uwa da wabi, lamarin da ya sa mazauna gujegujen neman tsira.
Ya shaida wa wa kafar talabijin ta Channels cewa wata tawagar ’yan banga, da shi kansa da wasu jami’an tsaro, suna sintiri a wani ƙauye ne lokacin da maharan suka kai harin.
Ko da yake jami’an tsaron sun yi artabu da maharan kuma sun yi nasarar fatattakar su, amma an riga an riga an kashe mutane talatin da shida nan take, wasu huɗu kuma suka mutu daga baya.
Wasu mazauna garin kuma sun samu raunukan harbin bindiga kuma suna samun kulawa a asibiti.
Hukumomin tsaro a jihar ba su yi wani sharhi ba game da harin, wanda ya zo ƙasa da makonni biyu bayan an kashe mutane hamsin da biyu a wasu ƙauyukan Karamar Hukumar Bokkos ta Jihar.