✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a gudanar da gasar wasannin makarantun Jihohin Kudu maso Yamma a Legas

Gwamnatin jihar Legas za ta karbi bakuncin gasar wasannin motsa jiki na makarantun sakandaren jihohin kudu maso yammacin Najeriya a watan Mayun shekarar nan da…

Gwamnatin jihar Legas za ta karbi bakuncin gasar wasannin motsa jiki na makarantun sakandaren jihohin kudu maso yammacin Najeriya a watan Mayun shekarar nan da muke ciki  (2014) wanda aka yi wa lakabi da DAWN a takaice.
Wata takardar sanarwar bayan taron kwanakin uku da masu ruwa da tsaki daga jihohin kudu maso yamma guda shida da suka hada da ma’aikatar wasanni ta kasa da cibiyar wasannin motsa jiki na makarantun kasa suka fitar ita ta nuna haka a karshen makon da ya gabata a Legas.
Takardar sanarwar wacce mai magana da yawun cibiyar wasannin motsa jiki na jihar Legas, Bashir Agunloye ya sanyawa hannu ta nuna cewa kalmar DAWN a takaice tana nufin Ajandar Bunkasa Jihohin Yamma na Najeriya.
Bashir Agunloye ya kara da cewa kalamar DAWN ta hada gwamnatocin jihohi shida na kudu maso yammacin Najeriya da suka hada da jihar Ogun da Oyo da Ondo da Ekiti da kuma jihar Legas don cimma wata muhimmiyar bunkasar tattalin arziki da zaman lafiya da hadin kai da  wassannin motsa jiki.
Sanarwar ta ce wasannin motsa jikin za su samar da wata kafa ta hada kan matasan yankin don nuna fasahar da suke da ita tare da kara musu kwarin gwiwar shiga wasanni daga kananan hukumomi.
Da yake jawabi a wurin taron, Darakta Janar na gasar, Dipo Famakinwa ya bayyana  muhimmancin wasanni  kuma ya bada tabbacin cewa cibiyar wasanni ta DAWN za ta yi aiki tukuru don tabbatar da nasarar wasannin.
Kwamishinan matasa da wasanni da walwalar jama’a na jihar Legas, Wahid Enitan Oshodi ta bayyana kokarin da gwamnan jihar  yake yi na ganin gasar wasannin ta sami nasara.
Gasar wasannin wacce za a gudanar daga ranar 16  zuwa 24 ga watan Mayun shekarar 2014 za ta hada da daliban karamar makarantun sakandare da kuma na babbar sakandaren jihohin Kudu maso yammacin Najeriya.
Gasar wasannin za ta hada da wasannin motsa jiji nau’i 12 da suka hada da wasan kwallon Kwando da kwallon badminton  da na kwallon kafa da ninkaya da kwallon tebur da kokawa da sauransu.
A hannun daya kuma taron ya tsara dokokin wasannin da shigar ’yan wasa da masu horar da su da lokaci da kuma yadda za a samu nasarar fara wasan da kammala shi cikin lokaci.