Gwamnatin Tarayya ta ce za ta gina wa akalla mutum 10,000 gidaje a gundumar Mosun da ke Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Kogi.
Gwamnati ta ce za a yi hakan ne saboda yadda Kogin Binuwai ke yin ambaliya a kowacce damina.
- ‘Kusan sau miliyan 13 aka yi yunkurin yi wa Najeriya kutse yayin zaben Shugaban Kasa’
- An baza ’yan sanda 18,748 saboda zaben Kano
Shugaban Hukumar Samar da Lantarki daga Ruwa (HYPPADEC), Abubakar Yelwa ne ya bayyana hakan yayin wani rangadi a yankin ranar Litinin.
Ya ce daukar matakin ya zama wajibi saboda mummunar barnar da ambaliyar ta yi a yankin a shekara ta 2022, inda dole sai da mazauna kauyen suka yi hijira baki daya don neman mafaka.
Ya ce, “Idan masu rike da sarautun gargajiya da kuma hukumomin Karamar Hukumar ta Bassa suka ba mu filin da za a yi aikin, nan da mako biyu za mu fara shi.
“Abin da muke fargaba shi ne sake aukuwar wata ambaliyar a bana, la’akari da hasashen da hukumar NiMet ta yi cewa a 2023, za a sami ruwan sama fiye da na bara, wanda hakan ke nufin akwai yiwuwar samun ambaliyar fiye da ya bara.
“Yanzu ga mu a wajen, kuma za ku iya gane wa idanunku irin barnar da ambaliyar ta yi a gundumar Mosun. Ya zama wajibi mu tashi tsaye wajen ceto rayuwarsu,” in ji shi.