✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a gama hanyar Abuja zuwa Kano nan da shekara biyu

’Yan Najeriya sun damu cewa wata 30 da fara aikin ba a yi rabinsa ba

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kammala aikin gyaran babbar hanyar Abuja-Kano kafin karshen wa’adin mulkin Shugaba Buhari na watan Mayun 2023.

Wannan jawabi daga Ma’aikatar Ayyuka da Gidajen tamkar da tufka da warwara ne, kasancewar a ’yan watannin baya Minista Babatunde Fashola, ya ce kammala aikin zai kai sheakrar 2025.

Ministan ya yi bayanin ne bayan Majalisar Tarayya da ’yan Najeriya suka koka kan tafiyar hawainiyar aikin, wanda ba wa kamfanin Julius Berger, ya kuma fara a watan Mayun 2018 da wa’adin wan Mayun 2021.

Wa’adin 2025 da ministan ya bayar a baya na nufin karin shekara hudu ke nan a kan wa’adin farko da aka sanya na kammalawa, shekara biyu bayan wa’adin mulkin Buhari.

Yanzu shekara biyu da rabi da fara aikin mai tsawon kilomita 375, amma ba a yi rabi ba, lamarin da ya sa ’yan Najeriya ke ta surutai a kai.

Mun gamsu da tafiyar aikin

Amma sanarwar da Mataimakin Daraktan Yada Labaran Ma’aikatar, Salish Badamasi, ya fitar ta ambato Daraktan Gyara da Gina Manyan Tituna, Funso Adebiyi, na cewa aikin na tafiya yadda ya kamata kuma cikin nasara.

Adeniyi ya yi bayani cewa da farkon aikin gyaran hanyar aka bayar, amma daga baya aka sauya aikin ya koma na gina sabon titin fil.

“Aiki ya yi nisa, an gina abin da ya fi kilomita 100 amma ba a wuri daya ba, a rukunin farko zuwa na uku (Abuja-Kano); an kammala kilomita 40 daga Kaduna zuwa Zaria, da kuma kilomita 70 daga Zaria zuwa Kano.

“Mun gamsu da ingancin aikin kuma muna kokarin ganin an kara saurinsa; kun shaida yadda aikin ke tafi a hannu biyun hanyar mai tsawon kilomita 375 daga Abuja zuwa Kano,” inji shi.

Tafiyar hawainiya

Da yake magana game da rashin saurin aikin, Adeniyi ya ce, “Yana da muhimmanci in yi gyara ga masu cewa aikin ba ya tafiya.

“Muna iya bakin kokari domin cika wa’adin da aka ba mu tare da tabbatar da ganin an yi aiki mai inganci yadda ya kamata.”

Ya ce gwamnati ta dukufa wurin ganin an kammala shi kuma tana bibiyar yadda yake tafiya a-kai-a-kai don magance duk matsalar da ta taso.

A nasa bangare, Daraktan Taswira ga Gina Gadoji na Ma’aikatar, Injiniya Adeoye ya yi kira ga kamfanin Julius Berger da ya kara hanzartawa ta hanyar sa karin ma’aikata a kowanne daga hannayen titin.