Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta sanar da cewa za a fuskanci matsanancin zafi da ya kai maki 40°C na tsawon kwana uku a wasu jihohin Arewa.
Hasashen, wanda Babban Daraktan Hukumar, Farfesa Mansur Matazu, ya sanya wa hannu, ya ce zafin zai haura maki 40°C a jihohin Kebbi da Sakkwato da Zamfara da Katsina da Kano da Jigawa, Bauchi da Gombe da Yobe da Borno.
- ’Yan bindiga sun kashe tsohon Kwamishinan Hukumar Kidaya
- Atiku ya sha alwashin yaki da matsalar tsaro in ya zama Shugaban Kasa
Ya bayyana cewa garuruwan Kebbi da Sakkwato da Katsina da Kano da Dutse da Nguru da Maiduguri za su iya fuskanci irin wannan matsanancin zafi tun daga ranar Lahadi.
Sanarwar ta ci gaba da cewa ana sa ran ranar Talata, 31 ga Mayu, 2022 jihohin Kebbi da Sakkwato da Zamfara da Katsina da Kano da Jigawa da Bauchi da Gombe da Yobe da Borno za su fuskanci zafi sama da 40°C.
Ya kara da cewa ana sa ran jihohin Neja da Filato da Abuja da Kwara da Kogi da Binuwai da Nasarawa da Taraba da Adamawa za su iya shiga yanayi na zafi daga tsakanin 35°C zuwa 40°C.