✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a farfado da wasan sukuwar dawaki a Jihar Kano

Shirye-shirye sun yi nisa wajen dawo da wasan sukuwar dawaki  Jihar Kano. Wannan jawabi ya fito daga bakin Shugaban Kungiyar Kula da Wasan Sukuwar Dawaki…

Shirye-shirye sun yi nisa wajen dawo da wasan sukuwar dawaki  Jihar Kano.

Wannan jawabi ya fito daga bakin Shugaban Kungiyar Kula da Wasan Sukuwar Dawaki ta Jihar Kano Alhaji Tajudden Dantata a lokacin da shugabannin kungiyar suka kai ziyara ga Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano Alhaji Ibrahim Galadima a ofishinsa.

Alhaji Tajudden Dantata ya bayyana cewa wasan sukuwar da suke son dawo da shi zai rika gudana ne duk  shekara wanda kuma zai zama ya yi gogayya da takwarorinsa na duniya.

Alhaji Tajuddeen ya bayyana cewa tun daga lokacin da aka ba su shugabancin kungiyar suka dukufa wajen ganin  an farfado da harkar wasan sukuwar dawaki a jihar inda suka fara shirya gasar sukuwar dawaki wacce ake yi a duk karshen mako.

“A bisa tunaninmu na son farfado da sukuwa  a yanzu haka muna gudanar da gasar sukuwa duk mako wanda kuma za mu dauki tsawon watanni shida muna gudanar da ita”.

Shugaban kungiyar ya bayyana cewa kungiyar ta fara daukara matakan gyaran babban filin sukuwa  da ke jihar  ta hanyar sake gina wasu vangarori na filin tare da samar da ruwa.

Kungiyar ta kuma roki Hukumar Wasannin da ta sahale mata ta yi amfani da wani sashe na filin wajen gina sakatariyar ta da kuma gina dakunan ajiye dawaki don a saukaka wa masu dawakin wajen sha’anin kulawa da su.

“Muna kuma neman izini wajen rage yawan kofofin shiga cikin filin  da kuma wurin ajiye motoci don samun cikakken tsaro a filin.”

Har ila yau kungiyar tana son ta gina karamar cibiyar wasanni da wurin motsa jiki da na shakatawa a babban filin sukuwar wanda zai samar da kudin shiga ga kungiyar da kuma  hukumar wasannin gaba daya.

Yayin da yake mayar da jawabi Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Galadima ya bayyana cewa gwamnatin Jihar Kano tuni ta bayar da kwangilar aikin gyaran filin sukuwar don ganin an samar da cikakken tsaro da tafiyar da wurin a tsare.

“Na san fiye da shekaru biyu gwamnati ta bayar da kwangilar gyaran filin, sai dai aikin ya tsaya wanda za mu bincika mu gano dalilin haka tare da ba gwamnati shawarar ci gaba da aikin don amfanin al’ummar jihar.”

Ya kuma nuna farin cikinsa game da aniyar da kungiyar ta dauka na farfado da wasan sukuwar dawaki a jihar, kasancewar wasa ne dama da jihar ta yi suna wajen gudanar da shi.