Gwamnatin Gombe ta kuduri aniyar farfado da wasan langa da kokawar gargajiya a tsakanin matasa domin dauke hankalinsu daga shaye-shaye.
Kwamishinan Matasa da Wasanni na jihar, Adamu Inuwa Ibrahim, ne ya shaida wa Aminiya hakan kan irin shirye-shiryen da suke da shi ga matasa a 2024.
Kwamishinan ya ce za su zakulo matasan da suke da baiwar iya wasanni musamman langa da kokawa da tsere da sauransu don ganin sun zamo masu amfani a tsakanin al’umma maimakon barin su suna shaye-shaye a kan titi.
Ya ce gwamna ya ba su damar hada kai da ma’aikatar ilimi wajen dawo da martabar wasanni a makarantun sakandare da ke fadin jihar.
A cewarsa gwamnati ta kuduri aniyar yin hakan ne ta hanyar ware wasu kudade a kasafin kudin 2024 domin ganin an bunkasa matasa wajen samar musu da sana’oi da kuma aikin yi baya ga wasanni.
Ya kuma ce gamsuwa da za a yi hakan ne ya sa wasu matasa sama da 50 suka gabatar da kansu a ofishin Kwamishinan ‘yan sanda suka kuma yi alkawarin taimakawa wajen hana barna a Gombe.
Sannan ya ce kamar wadanda ba sa zuwa makaranta za a samar da kwamiti da zai hada kai da hukumar wasanni wajen bi unguwa–unguwa ana zakulo su ana saka su cikin harkar wasanni sannan kuma a ga yadda za a yi su koma makaranta.
Wasu matasa da Aminiya ta zanta da su a jihar, sun ce muddin aka bullo da wannan shiri na wasanni za su shiga domin dama rashin abun yi ya sa suka shiga harkar shaye-shaye.
Sun ce harkar wasa abun sha’awa ne kuma ba sa haduwa da shaye-shaye, muddin mutum yana son ya yi suna har ya zama abun kwatance, sai ya ajiye shaye-shaye ya rungumi harkar wasanni da gaske.