Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya za ta fara tantance masu neman aikin kurtun dan sanda da sunansu ya fito ba yan sun yi rajista ta intanet.
Sanarwar da Kakakinta Frank Mba ya fitar a ta ce daga ranar 24 ga Agusta zuwa 6 ga Satumban 2020, za a tantance masu neman aikin da kuma takardunsu kai tsaye cibiyoyin da ta ware a fadin Najeriya.
Ya ce ana bukatar su halaci wuraren tantancewar sanye da farar riga T-shirt da gajeren wando kuma kowannensu ya zo da wadannan bayanai:
“Lambar shaidar dan kasa (NIN), takardar shaidar jarabawar kammala sakandare; takardardar shaidar zama dan karamar hukuma da kuma takardar haihuwa ko ta rantsuwar kotu kan bayanan shekaru.
“Za su jera dukkannin takardun bayanan a cikin fararen fayel guda biyu wadanda kowannesu ke dauke da hotunan fasfon mai su”, inji sanarwar.
Kazalika za su je da “takardar shaidar yin rajistar neman aiki da ta shaidar masu tsaya musu, in ba haka ba ba za a tantance su ba”.
Ya ce: “Za a yi tancecewar ne a cibiyoyi a dukkannin jihohi 36 da Birnin Tarayya wadanda nan gaba Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar zai sanar da bayanansu”.
Mba ya ce za a gudanar da dukkannin abubuwan da suka shafi tantancewar ne kyauta kuma a bayyane, cikin tsattsauran kiyaye matakan kare yaduwar COVID-19.
Rundunar ta shawarci masu neman aikin da su yi hattara da ‘yan damfara, tana mai barazar ta hukunta duk wanda ta kama da yunkurin damfarar masu neman aikinta.