Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta ce daga ranar tara ga watan Satumba za ta fara rijistar maniyyata aikin hajjin 2021.
Shugaban hukumar, Zikrullah Hassan a jawabinsa ga ‘yan jarida aAbuja ranar Alhamis ya ce hukumar za ta bude shafin intanet ga maniyyatan domin saukaka musu yin rijistar
“Muna shawartar maniyyata aikin hajjin bana da suka riga suka biya kudinsu kuma suke so a dawo musu da kudin amma ba su da asusun ajiya a banki da su gaggauta yin hakan”, inji Zikrullah.
Ya kara da cewa shirin adashin gata ga maniyyata na hukumar da aka dade ana jira zai fara aiki nan ba da jimawa ba.
Shugaban na NAHCON ya ce fashin gatan wani nagartaccen tsari ne da maniyyatan za su ji dadinsa matuka.
“Na yi amanna idan tsarin adashin gatan ya fara aiki zai saukaka hatta yawan kudaden da maniyyata suke biya domin aikin Hajji a nan gaba”, inji shi.
Sai dai ya yi kira ga maniyyatan da suke bukatar karbar kudadensu daga hukumomin alhazai na jihohi ko dillalai masu zaman kansu da su nemi yin hakan, yana mai cewar hukumar za ta tabbatar an biya su da gaggawa.
Ya ce tuni hukumar ta fara aikin mayar da kudaden ga hukumomin alhazan na jihohi.
Zikrullah ya ce maniyyatan da suka yanke shawarar barin kudinsu domin aikin Hajjin badi su za a fi bai wa fifiko a badin.
Hukumomin Kasar Saudiyya dai sun dakatar da aikin Hajjin bana ga baki daga wasu kasashen saboda tsoron annobar COVID-19.